A jiya Talata, gwamnatin jahar Bauchi ta sanar da cewa ta kashe Naira miliyan 96 wajen sayawa masarautun jahar dawakai a cikin shekaru biyu.
Kwamishinan kananan hukumomi na jahar, Nasurudeen Mohammed, shi ya bayyana haka a wani taron manema labarai a babban birnin jahar, Bauchi.
Ya ce masarautun jahar guda 6 Bauchi, Misau, Dass, Jamare, Katagum da Ningi su suka ci moriyar sayen dawakan.
Baya ga wannan, kwamishinan ya ce sun kashe naira miliyan 72.9 wajen yin takardar ‘yan asalin jaha iri daya a kananan hukumomin jahar guda 20.
Haka kuma ya ce an yi amfani da Naira miliyan 55 wajen ‘printing’ takardar shedar karbar kudi (wato Receipt) a kananan hukumomin guda 20.
Haka zalika kwamishinan ya ce gwamnatin ta kashe Naira miliyan 8.9 wajen shirya gasar kwallon kafa tsakanin kananan hukumomin.
Alkaluman da majalisar dinkin duniya ta fitar a 2015 dai ya nuna cewa kaso 86.6 cikin dari na mazauna jahar Bauchi na fama da talauci.
Mohammad, wanda shi ke shugabantar ma’aikatar da ke kula da ayyukan kananan hukumomi a jahar ya kuma shaida cewa gwamnatin ta biya wasu kudaden shari’a da basussuka da ake bin wasu daga cikin kananan hukumomin domin a kare martabar gwamnatin.
Ya ce kananan hukumomin sun hada da Shira, Alkaleri, Dambam, Misau, Bauchi, Giade da Toro.
Daga Alummata
Title :
Gwamnatin Jahar Bauchi Ta Kashe Naira Miliyan 96 Wajen Sayen Dawakai
Description : A jiya Talata, gwamnatin jahar Bauchi ta sanar da cewa ta kashe Naira miliyan 96 wajen sayawa masarautun jahar dawakai a cikin shekaru biyu....
Rating :
5