Sanata Shehu Sani mai wakiltar Kaduna ta tsakiya ya bayyana cewa sakon Barka da sallah da shugaba Buhari yayi da harshen Hausa ba wani kuskure ciki duk da cewa Nijeriya kasa ce mai yaruka da Yawa. Sani yace duk cece kuce da aka yi ana yi ne kawai amma Buhari na da ikon amfani da yaren da ya ga dama don turo wa jama'a sako a yanzu.
Sani yace tun da Buhari ya bawa Osinbajo wuka da nama wajaan tafiyar da kasa to bai kamata ayi tunanin zai yi magana da yaren kasa ba wajen turowa mutanensa sako ba.
A baya bayanan takardama ta kaure ganin yadda shugaba Buhari yayi amfani da yaren HAUSA wajen yiwa alummar musulmi Barka da salla kasantuwar ya kwashe fiye da kwana 50 yana jinya a birnin Landan.
Title :
Buhari Bai Yi Kuskure Ba Don Yi Wa Musulmi Barka Da Sallah Da Hausa
Description : Sanata Shehu Sani mai wakiltar Kaduna ta tsakiya ya bayyana cewa sakon Barka da sallah da shugaba Buhari yayi da harshen Hausa ba wani kusku...
Rating :
5