A ranar Larabar da ta gabata ne wasu suka yi garkuwa da mutane su ashirin a Titin Kaduna zuwa Abuja.
Barayin dauke da bindigogi sun kai su 30 kamar yadda wani direba da Allah ya yi zai tsira ya fadi.
Direban ya ce barayin sun yi ta tare motoci ne tun karfe 12:30 na rana inda suka tara su a waje daya kafin suka tafi da su cikin kungurmin daji.
Direban ya ce ya fadi ne a lokacin da suke tafiya amma ganin ya na neman ya suma sai sauran suka ci gaba da tafiya inda shi kuma Allah ya kwace shi ya rarrafa ya dawo kan babban titi in da ya shiga motarsa ya dawo Abuja don ya sanar wa ‘yan uwan wanda aka sace.
Majalisar wakilai ta nemi shugaban rundunar ‘Yan sanda Ibrahim Idris, Mai ba shugaban Kasa shawara a kan harkar tsaro, ministan tsaro Mansur Dan-Ali da su bayyana a gabanta domin yi mata bayani akan abinda ke faruwa a wannan hanya da yaki ci yaki cinyewa.
Tun ana dauka daya-daya yanzu dai gungu ake garkuwa dasu a hanyar Kaduna Zuwa Abuja.
Daga Rariya
Title :
An Yi Garkuwa Da Mutane 20 A Lokaci Guda A Titin Abuja Zuwa Kaduna
Description : A ranar Larabar da ta gabata ne wasu suka yi garkuwa da mutane su ashirin a Titin Kaduna zuwa Abuja. Barayin dauke da bindigogi sun kai su ...
Rating :
5