An maka wani matashi mai suna Mubarak Sa'idu a wata kotu da ke Abuja bisa zargin shiga zanga zangar neman a sako Shugaban Kungiyar Shi'a, Malam Ibrahim El Zakzaky.
Matashin, wanda dan asalin jihar Kano ne, an kama shi ne a yayin da suke shirin gudanar da tarzoman a masallacin Babban Birnin Tarayya Abuja ba tare da neman izini ba wanda hakan ya saba doka. Tuni dai ya musanta zargin amma Alkalin kotun, Mai Shari'a Umar Kagarko ya bayar da belinsa a kan Naira 100,000.
Title :
An Maka Wani Matashi Kotu Kan Shiga Tarzoman Neman Sako El Zakzaky
Description : An maka wani matashi mai suna Mubarak Sa'idu a wata kotu da ke Abuja bisa zargin shiga zanga zangar neman a sako Shugaban Kungiyar Shi...
Rating :
5