An yanke wa wani Malamin addinin Musulunci hukuncin ɗauri a kasar Saudiyya, saboda ya ɓata wa wani sanannen jarumin fim suna.
An yankewa Saeed bin Farwa hukuncin zaman kwana 45 a gidan yari, saboda ya kira Nasser al-Qasabi a matsayin "kafiri".
Malamai sun gudanar da wani gangami a kan Mista al-Qasabi don mayar da martani ga wata shahararriyar gidan talabijin inda jarumin kuma mai barkwanci ke yin ba'a ga kaifin kishin Islama.
Mista al-Qasabi ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa, wannan ya nuna cewa ba wanda ya fi karfin hukunci.
Title :
An Daure Malamin Addini Saboda Bata Wa Dan Fim Suna A Saudiyya.
Description : An yanke wa wani Malamin addinin Musulunci hukuncin ɗauri a kasar Saudiyya, saboda ya ɓata wa wani sanannen jarumin fim suna. An yankewa S...
Rating :
5