Daga Kwamared Zakari Y Adamu Kontagora
Sanata mai wakiltar Jihar Neja ta Arewa Dakta Aliyu Sabi Abdullahi (Baraden Borgu) kuma mai magana da yawun majalisar dattijan Nijeriya na fuskantar barazanar kiranye daga al'ummar mazabarsa.
A yau ne al'ummar mazabar Sanatan daga kananan hukumomi takwas suka fara zama na kokarin dawo da Sanatan gida, duba da yadda suka nuna rashin gamsuwar su da wakilcinsa.
Taron, wanda ya gudana a garin Kontagora, ya samu halartar al'umma da dama daga kananan hukumomi takwas da Sanatan ke wakilta.
Shugaban hadakar al'ummar dake yunkurin dawo da sanatan gida Alhaji Sahabi Mai Awaki, ya baiyana cewar ba su gamsu da irin salon wakilcin da Sanatan nasu ke yi masu ba, domin a cewar sa tun lokacin da suka zabeshi ba wani aikin cigaban al'umma da yayi masu, sannan ba wani kuduri na cigaban yankin nasu da ya taba gabatarwa a zauren majalisa, hatta ganinsa ma yayi masu wahala domin gaba daya ya kaurace masu ya koma Jihar Kwara wurin ubangidan sa Bukola Saraki.
Sahabi Mai Awaki ya kara da cewar duk kudurin da maigirma shugaban kasa Muhammad Buhari ya kawo wanda zai anfani al'ummar Nijeriya shine wakilan nasu ne a sahun gaba na kalubalantar wannan kudurin duk da alfarmar shugaban Buhari da ya ci a lokacin zabe, wanda ba hakan suka turashi yaje yi ba.
"Hakan ya sa muka ga dacewar mu dawo da shi gida ya huta mu tura mutumin da zai yi mana kyakkyawan wakilci nagari, mun kuma shirya tsaf domin ganin ya dawo gida da yardan Allah", inji shi.
Daga karshe shugaban ya yi kira ga al'ummar Neja ta Arewa da su basu hadin kai wurin ganin hakarsu ta cimma ruwa.
Rariya
Title :
Al'ummar Jihar Neja Ta Arewa Na Shirin Yi Wa Sanatansu Kiranye
Description : Daga Kwamared Zakari Y Adamu Kontagora Sanata mai wakiltar Jihar Neja ta Arewa Dakta Aliyu Sabi Abdullahi (Baraden Borgu) kuma mai magana ...
Rating :
5