Hukumar kula da hana yaduwar cutar kuturta ta kasa TLMN ta ce akalla mutane 4,000 ne ke kamuwa da cutar kuturta a kasa Najeriya duk shekara.
Shugaban hukumar Pius Sunday ne ya sanar da hakan da yake karanta jawabin sa a taron da hukumar ta shirya a jihar Sokoto mai taken ‘ Gudunmawar da kafafen yada labarai da zababbun ma’aikatan gwamnati za su iya baywarwa domin taimakawa masu dauke da cutar kuturta.’
Pius Sunday ya ce har yanzu cutar kuturta na addabar mutanen Najeriya musamman talakawa cikin su saboda rashin tsafta.
‘’Ya kamata gwamnati ta taimaka wa talakawa da tsaftattacen ruwa, abinci da ababen more rayuwa.
‘’Mafi yawa yawan mutanen da ke dauke da cutar ba sa samun abincin da zai taimaka wajen gina garkuwar jikinsu.’’
Pius Sunday ya yi kira ga gwamnati da su samar da shirye-shiryen da zai taimaka wajen kawar da talauci musamman a yankunan karkara wanda hakan zai hana yaduwar cutar.
Bayan haka shugaban hukumar kula da hana yaduwar cututtukan tarin fuka da zazzabin cizon sauro na jihar Sokoto Kabir Umar ya ce akalla mutane 160 ne ke dauke da cutar kuturta daga shekaran 2016 zuwa yanzu a jihar Sokoto.
Kabir Umar ya ce sun gano mutane 92 a shekaran bara a kananan hukumomin Kebbe, Gudu da Rabah sannan kuma sauran mutane 68 an gano su ne a wannan shekara.
Daga karshe ya yi kira ga mutne su daina kyamatar mutanen da kedauke da cutar kuturta.
Title :
Akalla Mutane 4,000 Ne Ke Kamuwa Da Cutar Kuturta A Kowace Shekara A Najeriya.
Description : Hukumar kula da hana yaduwar cutar kuturta ta kasa TLMN ta ce akalla mutane 4,000 ne ke kamuwa da cutar kuturta a kasa Najeriya duk shekara...
Rating :
5