Hukumar da ke yaki da cutar AIDS ko Sida ta jihar Kano, na neman majalisar dokokin jihar ta wajabta gwajin cutar kafin a yi aure.
A cewar hukumar, wata kiddiga da aka gudanar a bara ta nuna cewa kimanin kashi biyu bisa dari na mutanen da ke jihar na dauke da cutar ta Sida.
Sai dai hukumar ta ce duk da wannan kididdiga, adadin mutanen da ke kamuwa da cutar na raguwa a jihar.
Shugaban hukumar Dr Usman Bashir ya shaida wa BBC cewa, yin dokar zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar tsakanin ma'urata a jihar.
Ya kara da cewa, hukumar tana fadakar da jama'a a makarantu da sauran wurare kan yadda za su kaucewa kamuwa da cutar.
Daga BBC Hausa
Title :
Za A Yi Dokar Gwajin Ƙanjamau Kafin Aure A Jihar Kano
Description : Hukumar da ke yaki da cutar AIDS ko Sida ta jihar Kano, na neman majalisar dokokin jihar ta wajabta gwajin cutar kafin a yi aure. A cewar h...
Rating :
5