A cigaba da shirye shiryen mu na kiwon lafiya 1AREWA TV ofishin Red Cross ta jihar Bauchi a yanda tayi hira da Hajiya Khadijah Faruq, akan cutar Shartuwa ( Kyanda )
Ga Yanda Hira takaya
Hanyoyi Kariya Daga Cutar Kyanda
Ko me ke kawo ciwon kyanda kuma ko ya ake daukarsa? A kuma fada mana alamun ciwon da hanyoyin kariya. Na gode. Daga Musa Dudunni, Kusada
Amsa: Ciwon kyanda ko bakon dauro wani ciwo ne da a yanzu haka a wannan lokaci yara da yawa ke fama da shi saboda busasshiyar iska ta hunturu da rani da ke kadawa a Arewa. Wato su kwayoyin cutar iska suke bi sai a shake su idan an yi tari ko atishawa. Wasu kwayoyin cuta na ‘birus’ ne ke kawo ciwon. kwayoyin cutar sun fi kama yara ’yan kasa da shekaru biyar wadanda garkuwar jikinsu ba ta yi kwari ba. An kiyasta cewa a dan tsakanin wata biyu baya, yara fiye da 2,000 tuni sun riga mu gidan gaskiya a garuruwan Arewa da dama, sakamakon bullar ciwon.
Alamun ciwon su ne da farko yaro zai fara ciwo kamar mura, har idanu su rika yin ruwa suna ja, daga nan sai zazzabi, yaro ya kasa cin abinci. Daga nan sai a ga wasu kananan kuraje sun feso masa duk jikin, har baki. Wadannan kuraje sukan yi kaikayi sosai. Daga nan kuma ko dai jiki ya yaki kwayoyin cutar, ko kuma su ci gaba da jawo lahani. Misali, daga makogwaro har cikin kunne sukan iya shiga su kawo ciwon kunne. A ido ma sukan iya huda farin ido, idan suka shiga kirji kuma su kawo numoniya. Sai an dauki matakin karawa yaro kaifin garkuwar jiki kafin ya iya shawo kansu. Duk wannan yakan dauki misalin sati biyu yaro na fama. Yara masu karyayyar garkuwar jiki kamar masu ciwon kanjamau da ciwon suga ke nan sun fi shan wahala, tun da jikinsu yakan dau lokaci mai dan tsawo yana yakarsu.
Amma idan yaro yana da kwarin garkuwar jiki ba za a ma gane kyanda ba ce, domin ’yar mura kawai zai yi ta kwana uku zuwa hudu ya warke. Wasunsu ma ko murar ba sa yi, amma za su iya sa wa wani.
Hanyoyin kariya daga wannan cuta kan fara tun daga lokacin da aka haifi yaro. Idan aka ba jariri nonon uwa zalla har wata shida ba ko ruwa, to garkuwar jikinsa za ta fi ta sauran yara karfi, ta yadda ba zai rika cutuka sosai ba. Sai kuma allurar riga-kafin ita kwayar cutar da ake yi a wata tara. Yawanci wadanda suke yin ciwon ba a yi musu allurar riga-kafin ba.
Sauran hanyoyin kariya sun hada da saurin kai mai ciwon asibiti da ware masa wurin kwanciya daban da na sauran yaran gida don kada ya yada musu da samar masa soson wanka nasa na daban don kada ruwan majina ko na kurajen jikinsa su sa kwayoyin cutar a jikin soson. Sai kuma yawan wanke hannayen yaran gidan da sabulu. Ko makaranta mai ciwon bai kamata ya je ba tsawon ’yan wadannan kwanakin da yake ciwon, don kada ya yada ta.
Shin mene ne ciwon gonorrhea kuma wane magani ne ko allura mai ciwon sanyi na gonorrhea zai yi amfani da shi kafin ya kai ga zuwa asibiti?
Daga danmaryam, Kebbi
Amsa: To bari a ba dalibin likita, Umar Musa Gwadabawa fagen ya amsa maka tambayar taka, inda ya ce: Ciwon sanyi na ‘gonorrhoea’ cuta ce da ake samu daga mace zuwa namiji ko namiji zuwa mace. kwayar cutar bacteria mai suna Neisseria Gonorrhoea ke kawo ciwon. kwayar tana rayuwa a wuri mai danshi da ruwa a jiki kamar a mahaifa, ko mafitsara, haka kuma a baki da ido.
daukar cutar a ido kan faru ne a jarirai, idan jariri ya kwashi kwayoyin cutar yayin haihuwa a kwararon hanyar fitowa duniya. A wannan lokaci ne za a ga idanun sabon jariri na kwantsa, yana ja. Idan a gida aka haihu, dole a kai jariri asibiti a ba shi magani, saboda kwayar cutar kan jawo makanta.
Ba a daukar cutar sanyin ta hanyar musabaha ko zama a bayan gida inda mai cutar ya zauna.
Wadanda suka fi zama cikin hadari ke nan su ne masu mu’amala da mata masu zaman kansu, domin mata su ke da kwayar cutar amma ba wasu alamun cuta a jikinsu da za a gane sai an yi gwaji.
Alamomin cutar ke nan sun bambanta daga mace zuwa namiji. Mafi yawan mata masu cutar ba su cika nuna wata alama ba. Amma a maza wadanda ke nuna alama takan bayyana bayan kwana goma da kamuwa. Ga alamomin kamar haka:
1-Ciwo ko jin zogi lokacin fitsari. 2-Ganin farin ruwa karshen fitsari. 3-Kumburi ko ciwo ga ’yan maraina. Da zarar an ga wadannan alamu sai a gaggauta ganin likita.
Gwajin da ake yi domin gano cutar, kuma wanda ya kaamata a yi wa duk wanda ake tunanin yana fama da ciwon, sun hada da: 1-daukar farin ruwan a kai dakin gwaji domin a gwada. 2-Sai kuma gwajin fitsari. Za ka iya zuwa asibiti a yi maka wannan gwaji idan kana tsammanin kana dauke da kwayar cutar.
Maganin cutar ya danganta da irin karfinta a jikin mutum, domin akwai har allurai ma, kuma sai ma’aikacin asibiti ya rubuta. Don haka ba kai za je ka sawo magani ka sha ba. Idan aka ba da maganinta ga mutum, to ya tabbata ya sha na tsawon lokacin ko da ya ji sauki kafin su kare.
Matsalar cutar kan yi muni idan aka ki daukar matakin magance ta. Tana kawo matsaloli da yawa ga mata kamar: 1-Jawo mummunar illa ga kwayoyin halitta masu kula da haihuwa, wadanda ke haddasa rashin daukar ciki. 2-Yiyuwar yaduwar cutar zuwa wasu bangarori na jiki. 3-Yiyuwar kamuwa da cutar kanjamau. 4-Lokacin da aka samu juna biyu matar da ke dauke da cutar sanyi kuma ba a yi maganinta ba, takan haifar da barin juna biyun. 5-Haka kuma abin da ke cikin cikinta kan kamu da cutar ta ido, lokacin haihuwarsa.
Hanyoyin da ya kamata ma’aurata su bi wajen kariya daga cutar su ne: 1-Zama masu amana tsakanin juna. 2-Kada a ji kunyar zuwa ganin likita. 3-Masu juna biyu su je awo inda za a yi musu gwajin cutar. 4-A yi kokarin shanye dukkan magungunan da aka bayar a asibiti. 5-Ga mai iyali fiye da daya, yana da kyau idan yana dauke da cutar to ya je da dukkan iyalin domin a yi musu gwaji. Gwaji a mata ita ce kawai hanyar da ake gane ciwon. 6-Sa’annan kuma kada a yi mu’amala da mai cutar har sai ya warke.
Ina tambaya akan yankan farce da ake yi wa mutane. Na kan ga idan aka gama yankewa wani sai a kunna wuta a kona bakin almakashin kafin a yi wa wani kuma. To hakan ba zai sa a dauki cutar kanjamau ba ke nan? A yi min karin haske.
Daga Matar Soja
Amsa: E, duk lokacin da aka sa wuta a jikin wani karfe na dan lokaci ana iya kashe kwayoyin cutar da ke jikinsa, har kwayar cutar kanjamau kuwa. Don haka ne ake cewa masu yankan farce dole ne su gasa abin yankansu duk bayan yi wa kowane mutum, domin kiyaye yada cututtuka.
Duk lokacin da na yi tukin mota na yi ’yar tafiya mai dan nisa kamar kilomita 90, to da na sauko daga motar sai in ji na gaji, kafafuwana wani lokacin sai su rika mani ciwo har sai na kai ga dangyashi kafin su warware.
Daga Aminu M. Mai’aduwa
Amsa: E, ai dama cewa muka yi dole ka rika fita kana mike kafa idan kana samun irin haka. Muka ce akwai mutanen da ’yar tafiya kadan idan suka jima a zaune dole su ji wannan minjiryar ta rike kafa, musamman ma idan suna da nauyi sosai. Ba ciwo ba ne domin da ka tsaya da motar ka fito ka dan taka abin zai sake ka. Duk lokacin da mutum ya ji hakan ko kilomita ashirin ne, ya fi kyau a fito a mike kafa a koma.
Mene ne gaskiyar da ake cewa idan gashin kyanwa ya shigar wa mutum baki yana kawo tari na fitar hankali?
Daga Ali Fancy, Garko
Amsa: A’a, ba gaskiya a zancen. Akwai dai mutanen da ke samun borin jini idan wani abu kamar kura ko gashin kyanwa ko na wata dabba ko tsinken karmami ya shiga hancinsu ba bakinsu ba, ciwon da ake kira ‘hay feber’ wanda kan sa hanci kaikayi ya kawo mura mai zafi wadda ba ta tafiya cikin sauki. Duk da cewa mu ma mukan samu ciwon amma dai an fi samun borin jini mai tsanani a tsakanin Turawa, ba bakake ba.
Wai shin da gaske ne yawan kwanciya a kan dabe na ‘tiles’ yana kawo ciwon nimoniya?
Daga Baban Kulu, Lafiyan Bare-Bari
Amsa: Numoniya ciwo ne da kwayoyin cuta kan kawo ba sanyi ba. Da sanyi ne ke kawo shi da mutanen kasashen da ake sanyi sosai wanda ya fi namu tuni sun kare da numoniya. A kwayoyin cututtukan da ke sa ciwon numoniya (tunda suna da yawa) akwai wadda dai ta fi son sanyi da danshi.
Daga Aminiya
Title :
Video: KIWON LAFIYA - Bayani Kan Cutar Kyanda Tare Da Hajiya Khadijah Faruq
Description : A cigaba da shirye shiryen mu na kiwon lafiya 1AREWA TV ofishin Red Cross ta jihar Bauchi a yanda tayi hira da Hajiya Khadijah Faruq...
Rating :
5