...'Yan Nijeriya ku kwantar da hankalinku ciwo na bai yi tsanani ba, kuma ina godiya da addu'o'in da kukr yi min, cewar shugaba Buhari
A daren Lahadi ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sake shillawa kasar Ingila domin sake duba lafiyarsa, kamar yadda mai taimakawa shugaban kasan kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya tabbatar.
Tun da ranar yau shugaba Buhari ya so tafiyar amma sai ya daga tafiyar zuwa daren yau sakamakon karbar bakoncin 'yan matan Chibok din da Boko Haram suka sako da zai yi.
Shugaba Buhari ya kuma bada sako ga 'yan Nijeriya cewar kada su tada hankalinsu domin ciwon dake damunsa bai yi tsanani ba. Kuma yana mika godiyarsa ga daukacin al'ummar Nijeriya bisa addu'ar da suke yi masa kan rashin lafiyarsa.
Adadin tsawon kwanakin da shugaba Buhari zai yi a yayin tafiyar, ya danganta ne da kwanakin da likitocin za su yanke masa.
Tuni dai shugaba Buhari ya rubuta wasikar tafiyar tasa ga majalisa domin sanar da su kamar yadda dokar kasa ta tanadar.
Title :
Shugaba Buhari Ya Shilla Birnin Landan A Daren Jiya Domin Sake Duba Lafiyarsa
Description : ...'Yan Nijeriya ku kwantar da hankalinku ciwo na bai yi tsanani ba, kuma ina godiya da addu'o'in da kukr yi min, cewar shugaba...
Rating :
5