Uwargidan Shugaban Najeriya, Aisha Buhari ta ce ana zuzuta rashin lafiyar mijinta fiye da kima.
A sakonnin da ta wallafa a shafinta na Twitter uwargidan shugaban kasar ta ce Shugaba Muhammadu Buhari mai shekara 74 yana ci gaba da aikinsa da kuma ganawa da manyan jami'an gwamnati.
"Gaskiya ciwon bai yi tsananin da mutane ke zuzuta shi haka ba, don kuwa yana tafiyar da duk al'amuransa da ya saba," in ji Aisha Buhari.
Ta kuma yi godiya ga 'yan Najeriya kan yadda suka nuna damuwarsu da soyayyar da addu'o'i kan rashin lafiyar mijin nata. Wasu masu fafutuka a Najeriya sun bukaci shugaban kasar ya dauki hutun jinya yayin da ake kara nuna damuwa kan lafiyarsa.
Title :
Rashin Lafiyar Buhari Bai Yi Tsanani Yadda Ake Zato Ba - Aisha Buhari
Description : Uwargidan Shugaban Najeriya, Aisha Buhari ta ce ana zuzuta rashin lafiyar mijinta fiye da kima. A sakonnin da ta wallafa a shafinta na Twi...
Rating :
5