Jama'a gini akan hadisin da Annabi alaihissalam yace : musulmai kamar gini guda suke, sashinsu yana karfafar sashi, idan gaba daya ta kamu da ciwo duka gangar jiki sai fara daukar zazzabi da masasshara.
Dogaro da wannan hadisi muke sanar da al'umma, akwai yaro qaninmu dalibin ilmi hafizin Alqur'ani da yake fama da ciwon koda, wanda a yanzu haka yana asibitin Nassarawa ana yi mishi wankin koda (dialysis ) sau biyu a sati, ga ciwon ya yi tsananin da sai an fita da shi waje an yi mishi dashen koda, wanda ake neman zunzurutun kudi dalar Amurka 13500 wanda a canjin kudin Nieriya ya doshi miliyan goma, kuma karfin mu ya yi kasa don haka muna neman taimakon 'yan uwa gwargwadon ikon kowa.
Sunan yaron: Nayif Isma'il, dan Fagge ne layin malam Umar sani Fagge, malami ne mai koyar da Alqur'ani a makarantar Ansarussunnah Fagge ,
Ga mai bukatar taimakawa da abinda Ya samu ga account din yayanshi Shakeeki kamar haka:
Account name: Assad Isma'il Zakariyya,
Bank: first bank,
AccNo: 3019347746
Acctype: saving.
Title :
Photos: Mahaddacin Kur'ani Na Bukatar Agajin Gaggawa
Description : Jama'a gini akan hadisin da Annabi alaihissalam yace : musulmai kamar gini guda suke, sashinsu yana karfafar sashi, idan gaba daya ta k...
Rating :
5