Daga Zuma Times Hausa
Kimanin shekaru 15 da kaddamar da shariar Musulinci a jihar Jigawa wanda ya haifo da kafuwar rundunar Hisba a jihar.
Wakilimmu na jihar Jigawa ya yi kicibis da inda ake holewa a kasuwar Gujungu da ke karamar hukumar Taura inda makada, mawaka da 'yan chacha dama karuwai suke baje kolin kayan masha'a a bainar jama'a a ranar kasuwar ta Gujungu.
Hakan ya jawo cheche-…kuce a tsakanin jama'a inda suna cewa gwamnati da hukumar Hisba sun kasa aiwatar da aikinsu sun daina komai a kasuwannni sai kawai kamen 'yan D.J da kuna takura wa jama'a.
Wata yarinya mai karancin shekaru mai wadda ta ce subanta Hadiza Usman, ta bayanna cewa daga Damaturu ta ke zuwa duk sati ta yi sana'ar karuwanci ta koma gida kuma tana zuwa kasuwar Gujungu saboda ba a kama su kuma in har an kama su tana da wadanda za su yi belinta
Hadiza ta kara da cewa ita fa ba za ta daina karuwanci ba saboda an kashe iyayenta a lokacin fadan boko haram inda ta ce, tana yin karuwanci ne domin babu yadda za ta yi ta rayu tunda ba ta da wata sana'a kuma ta rasa wanda zai aure ta yar ufa mata asiri.
Shi kuwa wani mai sana'ar gurmi nema a rufamar asiri kada a bayyana sunansa ya ce, ya kai shekara 26 yana sana'ar gurmi babu irin kudin da bai rike ba amma yanzun ya dawo gida daga Abuja saboda rusau da ministan Abuja ya yi har ya hada da gidajansu.
"Shi fa Allah ne bai kira ni Makkah ba da tuni na sauke farali domin ina da kudin zuwa amma Allah bai nufa ba kuma yanzu haka ina da mata hudu da 'ya'ya 26 ina da motar hawa da gidana a nan Gujungu amma duk da wannan samayya ba ni da burin a ce 'ya'yana sun yi sana'ar kida/"
Ya ce, sana'ar gurmi ba ta da tsafta domin yana kida ne karuwai suna rawa amma zuwansa jihar Jigawa sun hana su neman abinci suna kama su suna danne masu hakki wanda bai kamata ace ana yi masu hakan ba.
Da ya ke amsa tambayoyin Zuma Times shugaban hukumar Hisbah ta Jihar Jigawa, Alhaji Aminu Baba Waziri ya ce, za su kai sammame kasuwar za kuma su kama duk wadda suka kama a gidan giyar sannan su gurfanar da su a gaban kotu.
Ya kara da cewar ya jima yana jin labarin irin fasadin da ake aikatawa a kasuwar ta Gujungu har ma ana cewa ba su yin aiki amma za su dauki mataki.
©Zuma Times Hausa
Title :
Photos: Karuwai, Makada Da 'Yan Chacha Sun Mamaye Kasuwar Gunjugu Ta Jihar Jigawa
Description : Daga Zuma Times Hausa Kimanin shekaru 15 da kaddamar da shariar Musulinci a jihar Jigawa wanda ya haifo da kafuwar rundunar Hisba a jihar...
Rating :
5