.
Masu tada kayar baya a kasar Somaliya sun jefa wani magidanci har sai da ya mutu bayan wata kotun ta same shi laifin aikata zina.
An binne marigayin mai suna, Dayow Mohamed Hassan ne iya wuya, inda daga nan mayakan al-Shabab suka rika yi masa ruwan duwatsu har sai da ya mutu.
Daruruwan mutane ne suka taru a lokacin da ake zartar da hukuncin a kauyen Ramo Adey da ke lardin Bay da ke kasar Somaliya.
Al-Shabab ta samu Dayow, mai shekara 44 ne da laifi yi wa wata mata ciki, duk da cewa yana da mata biyu, kamar yadda hukumomi suka bayyana.
Kungiyar al-Shabab ta saba yanke irin wannan hukunci a yankunan da suke karkashin ikonta a kasar.
A shekarar 2014, kungiyar ta jefe wani yaro har sai da ya mutu bayan ta same shi da laifin yi wa wata mata fyade. Hakazalika, an kashe wata yarinya matar aure a irin wannan hukuncin bayan da suka same ta da laifin aikata zina.
Title :
Photos: An Jefe Magidanci Har Lahira Saboda Yin Zina A Somaliya
Description : . Masu tada kayar baya a kasar Somaliya sun jefa wani magidanci har sai da ya mutu bayan wata kotun ta same shi laifin aikata zina. An bin...
Rating :
5