Shahararren kamfanin nan mai shirya fina-finan Hausa Abdul Amart Maikwashewa, ya saki tirelan sabon fim din da ake ta jira mai suna SULTANA.
Sultana dai fim ne da ya kunshi Shahararru kuma jaruman ‘yan fim da ya hada da Jaruma Nafeesat Abdullahi,
Wannan fim dai anayi masa kirari da ‘Kamar Ba A Taba Yin Irinsa Ba’ tun kafin ya fito ganin irin jaruman da suka fito a fim din.
Abdulamart ya saka wannan tirela ne a shafinsa na Instagram.
Jaruman da suka fito a fim din sun hada da Sarki Ali Nuhu, Wassh Waziri,Hauwa Maina, Adam Zango da dai sauransu.
Wasu daga cikin wadanda suka kalli tirelan sun yabi irin jarumtakar Nafeesat Abdullahi a fim din.
Ameera Yunus ta zanta da wakilinmu inda ta ce Nafeesat ta kure jarumtaka a wannan fim din kuma ana neman a shiga hakkinta wajen jiran fim din.
” Duk da Nafeesat jaruma ta ce da nafi so a farfajiyar fina-finan Hausa, wannan karon ta kure ni domin tirelan Sultana kawai ya gama dani. A gaskiya an ja mana rai da wannan tirela amma mana nan muna jira.”
Premium Times Hausa
Kalli Talla Fim Din SULTANA
Title :
Photos: Ba Kowace Jaruma Bace Zata Iya Yin Abin Da Nafeesat Tayi A Fim Din SULTANA.
Description : Shahararren kamfanin nan mai shirya fina-finan Hausa Abdul Amart Maikwashewa, ya saki tirelan sabon fim din da ake ta...
Rating :
5