A ranar Talata ne uwargidan shugaban kasar Najeriya Hajiya Aisha Buhari ta tafi Birtanyia domin duba mijinta da yake ganin likita a birnin London.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewa Hajiya Aisha ta yi tafiyar ne a ranar Talata da safe, inda ta tashi ta filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Kafin tafiyar tata dai Hajiya Aisha ta mika godiyarta ga 'yan Najeriya a bisa goyon bayan da suke bai wa mijinta Shugaba Muhammadu Buhari.
Sai dai kuma babu wani bayani da ke nuna ranar da za ta dawo daga tafiyar, kamar dai yadda ba a san ranar dawowar mijin nata ba.Shugaba Buhari dai ya koma London ne a karo na biyu cikin wanann shekarar a ranar 7 ga watan Mayu, domin likitoci su sake duba lafiyarsa
Sai dai rashin lafiyar shugaban tana janyo ce-ce-ku-ce sosai a kasar, inda wasu ke ganin kamata ya yi shugaban ya yi murabus ya fuskanci kula da lafiyarsa.
Amma wasu kuwa suna ganin tun da ya mika ragamar shugabanci a hannun mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, to babu wani abin damuwa.
Har yanzu dai ba a san takamaimai cutar da ke damun Shugaba Buhari ba.
BBC Hausa
Title :
Photos: Aisha Buhari Ta Tafi Landan Ganin Mijinta
Description : A ranar Talata ne uwargidan shugaban kasar Najeriya Hajiya Aisha Buhari ta tafi Birtanyia domin duba mijinta da yake ganin likita a birnin L...
Rating :
5