...Zai kuma gana da 'yan kasuwa a kan kalubale da suke fuskanta
Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo zai kaddamar da asibitin matsakaita da kananan masana'antu (MSMEs) a yau Alhamis, a jihar Katsina a yunkurin bunkasa tattalin arziki da ayyuka a kasar nan.
Kwamishinan ciniki, masana'antu da yawon shakatawa na jihar Katsina, Alhaji Abubakar Yusuf ne, ya sanar da hakan a lokacin da yake jawabi ga manema labarai a Katsina a jiya Laraba.
Kwamishinan ya ce a lokacin ziyarar, Osinbajo zai gana da 'yan kasuwa a kan kalubale da suke fuskanta da kuma yadda za a shawo kan matsalolin.
Yusuf ya ce gwamnatin jihar ta riga ta kafa wani kwamiti don wayar da kan 'yan kasuwa a kan muhimmancin ziyarar.
Daga Rariya
Title :
Osinbajo Zai Ziyarci Jihar Katsina Don Kaddamar Da Asibiti
Description : ...Zai kuma gana da 'yan kasuwa a kan kalubale da suke fuskanta Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo zai kaddamar da asibitin matsa...
Rating :
5