Ofishin Hukumar kwastan mai kula da jihohin Kano da Jigawa ya kama wata motar terala dauke da buhunan shinkafa ‘yar kasashen waje 377 tare da wasu kayayyaki.
Kwamandan Hukumar mai kula da jihohin biyu, Mr. Abutu Onaja, ya sanar da hakan ga manema labarai a Dutse.
Ya ce jami’ansa ne suka kama motan mai dauke da kayayyakin a kusa da Birnin Dutse
Kari da cewa, motar make da shinkafar ‘yar kasar wajen bahu 377 da bahunan dabino da na sukari da kuma tayoyi da aka yi amfani da su.
Mr. Onaja ya kara da cewar kayayyakin an musu kudin fito akan N4,100,000.
Sai dai yace direban motar ya ranta ana kare yayinda babu wanda suka kama ya zuwa yanzu
Ya ce, a bara hukumar ta bada shinkafa bahu 4220 da ta kwace ga yan gudun hijra
Title :
Hukumar Kwastam Ta Kama Buhunan Shinkafa 377
Description : Ofishin Hukumar kwastan mai kula da jihohin Kano da Jigawa ya kama wata motar terala dauke da buhunan shinkafa ‘yar kasashen waje 377 tare d...
Rating :
5