Wani dan kwallon kungiyar kwallon kafa ta Kwara United Saka Azeez ya yanke jiki ya fadi a jiya Juma'a a filin wasa na Ilori a yayin da suke kan gudun motsa jiki a shirin wasan gasar firimiyar Nijeriya da ake bugawa.
Mahaifinsa Kasali Lasisi shahararren dan wasan kwallon Tabur ne ‘Table Tennis’ wanda gwamnatin jihar Kwara ta karrama a kwanakin nan.
Kakakin kungiyar kwallon kafan yace abin ya ba su tsoro domin suna gudun motsa jiki ne kawai sai ya yanke jiki ya fadi.
“Da yake muna kusa da asibiti ne sai muka dauke shi ranga-ranga zuwa can. Bayan likitoci sun duba shi sai suka sanar mana cewa ya riga ya cika.”
Kungiyar kwallon kafa na Kwara United sun siyo Azeez ne daga Zamfara United a farkon wannan shekarar kwallo wato 2017/2018.
Title :
Graphic Photos: Dan Kwallon Kwara United Ya Mutu A Filin Wasa
Description : Wani dan kwallon kungiyar kwallon kafa ta Kwara United Saka Azeez ya yanke jiki ya fadi a jiya Juma'a a filin wasa na Ilori a yayin da...
Rating :
5