Rundunar ‘yan sandan jahar Kano ta fitar da sanarwa ta musamman da ke bayyana dalilin ta na kama tsohon gwamnan jahar Jigawa Alhaji Sule Lamido.
A sanarwar, wacce mai magana da yawun rundunar Samba Sokoto ya fitar, ya bayyana cewa sun samu korafi da ke nuna cewa Lamido ya yi wasu maganganu da za su iya ingiza magoya bayan sa su yi tashin hankali.
Ya ce a ranar 27 ga watan nan ne suka samu korafin daga gwamnatin Jigawa, inda aka zargi Lamido da ingiza magoya bayan sa da nufin su yi tashin hankali a zaben kananan hukumomi da za a yi a ranar 1 ga watan Yuli.
A fadarsa, wannan laifi ya saba wa sashi na 114 na kundin dokar ‘Penal code’. A don haka su na kan bincike akan batun kuma za su mika Lamido ga kotu da zaran sun kammala.
Daga Allummata. com
Title :
Dalilin Da Ya Sa Muka Kama Sule Lamido – ‘Yan Sanda
Description : Rundunar ‘yan sandan jahar Kano ta fitar da sanarwa ta musamman da ke bayyana dalilin ta na kama tsohon gwamnan jahar Jigawa Alhaji Sule Lam...
Rating :
5