Daga Jaridar Rariya
An yi garkuwa da Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Sumaila/Takai dake jihar Kano, wato Honarabul Garba Durbunde.
Majiyarmu ta Daily Nigerian ta rawaito cewa dan majalisan ya baro Abuja zuwa Kano ne da misalin karfe biyar na yammacin jiya Talata amma sai masu garkuwa da shi din suka tare shi a daidai Jere.
Majiyar ta kara da cewa shi kadai ne a cikin motar a yayin da aka yi garkuwa da shi.
Wasu takwarorinsa guda biyu da aka ji ta bakinsu kan lamarin, sun tabbatar da aukuwar hakan, amma suna kan bincike.
Title :
An Yi Garkuwa Da Wani Dan Majalisar Tarayya
Description : Daga Jaridar Rariya An yi garkuwa da Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Sumaila/Takai dake jihar Kano, wato Honarabul Garba Durbu...
Rating :
5