Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya yi ikirarin cewa akwai kyakkyawar dangantaka tskaninsa da Shugaba Muhammad Buhari sabanin yadda ake yayatawa a kafafin Sada zumunci.
Saraki ya bayyana haka ne a lokacin da wata tawagar Kungiya Izala a karkashin jagorancin Muhammad Jingir da kai masa ziyara a Abuja inda ya tabbatar wa tawagar ci gaba da bayar da cikakken hadin kai ga Shugaba Buhari.
A nasa jawabin, Shugaban tawagar, Muhammad Jingir ya yabawa Saraki bisa rawar d ya taka ta yadda aka samu Shugaban kasa Musulmi kuma Mataimakinsa, Kirista inda ya nuna cewa akwai bukatar yin adalci a tsakanin mabiya addinan biyu.
Title :
Akwai Kyakkyawar Alaka Tsakanina Da Buhari - Saraki
Description : Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya yi ikirarin cewa akwai kyakkyawar dangantaka tskaninsa da Shugaba Muhammad Buhari sabanin ya...
Rating :
5