Daga Kwamared Zakari Y Adamu Kontagora
A safiyar yau ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gurfanar da tsohon gwamnan Neja Dakta Mu'azu Babangida Aliyu da tsohon kwamishinan muhalli kuma shugaban ma'aikata na jihar Neja sannan dan takarar gwamnan Neja a jama'iyar PDP Alhaji Umar Nasko a gaban babban kotun taraiya dake Minna fadar gwamnatin jihar bisa zargin su da kuruciyar bera da makuddan kudade kimanin naira biliyan 3.
Hukumar EFCC ta baiyana cewar Aliyu wanda aka fi sani da hadimin al'umma (Chief Servant) ya karkatar da N520m daga asusun tsaro na gwamnatin jihar zuwa asusun ajiya na bankin Zenith daga watan janairu zuwa maris na 2011, a wannan lokacin kuma tsohon gwamnan ya kara karkatar da N1.7b zuwa wannan asusun.
Hukumar ta kara da cewar a shekarar 2015 Aliyu da Nasko sun karkatar da Naira biliyan 1.09 daga kaso 16 da kamfanin Samar da wutan lantariki na North South Power Company Limited yake baiwa jihar, laifin da hukumar ta ce ya sabawa sashi na 97 da sashi na 312 na kundin laifuffuka na final kot.
Zarge zarge guda 6 hukumar ta EFCC ke karar tsohon gwamnan da Umar Nasko da aikatawa, zargin da suka musanta agaban kotu.
Bayan tafka dogon muhawara, Lauyan wadanda ake zargin ya nemi kotu ta bada belin su, bukatar da lauyan EFCC ya ki amincewa da shi, daga karshe mai shari'a Maiyaki ya bada umarnin a ci gaba da tsare Babangida Aliyu da Umar Nasko a sabon gidan yarin Minna har zuwa ranar 3 ga watan Mayu, 2017.
Rariya
Title :
Yadda EFCC Ta Gurfanar Da Tsohon Gwamnan Neja Da Tsohon Dan Takarar Gwamna A Kotu
Description : Daga Kwamared Zakari Y Adamu Kontagora A safiyar yau ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gurfanar da tsohon gwamnan Neja Dak...
Rating :
5