Rundunar Sojan Nijeriya ta tabbatar da cewa ta gano makamai a Kudancin Kaduna a ci gaba da kokarin da take yi na samar da zaman lafiya a yankin sakamakon rikice rikicen da suka yi sanadiyyar salwantar da rayuka da dama.
Kakakin Rundnar, Sani Usman ya ce an gano makaman ne a ya yin wani bincike da rundunar ta yi a garuruwan Gwaska, Angwan Far, da kuma Bakin Kogi da ke Kudancin jihar inda ya ce za a fadada aikin zaman lafiyar a dazuzzukan jihohin Bauch, Kano da Plateau.