...sun farfafasa masa mota da gida
Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Gamawa dake jihar Bauchi, Honarabul Garba Mohammed Gololo ya sha da kyar a hannun wasu mafusatattun matasa dake mazabarsa a yayin da ya kawo wata ziyara yankin nasa. Majiyarmu ta rawaito mana cewa lamarin ya auku ne a ranar Lahadin da ta gabata.
A yayin da dan majalisar ya kawo ziyarar yankin Gololo, mafusatan matasan sun yi ta jifan dan majalisan har ta ga sun farfasa masa mota da gida. Daga bisani ya gudu zuwa yankin Gamawa, inda nan ma rahotanni sun nuna cewa bai tsira daga fushin matasan yankin ba.
Idan za a iya tunawa, Honarabul Garba Gololo, yana daga cikin 'yan majalisu guda uku da aka zarge su da yunkurin yin fyade a yayin wata ziyarar aiki da suka kai kasar Amurka a shekarar da ta gabata, wanda hakan ya jawo cece-kuce har ta ga majalisar wakilai ta kafa kwamiti na musamman domin gudanar da bincike kan lamarin.
Title :
Mafusata Sun Yi Wa Dan Majalisar Tarayya Ruwan Duwatsu A Bauchi
Description : ...sun farfafasa masa mota da gida Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Gamawa dake jihar Bauchi, Honarabul Garba Mohammed G...
Rating :
5