Daruruwan masu zanga-zanga sun taru a kofar shiga majalisar dokoki, da ke babban birnin tarayya Abuja, inda suke neman a janye dakatarwar da aka yi wa Sanata Ali Ndume wanda ke wakiltar Borno ta Kudu.
A makon da ya gabata ne majalisar dattawan kasar ta dakatar da Sanata Ndume har tsawon wata shida, saboda korafin da ya gabatar kan shugaban majalisar da kuma Sanata Dino Melaye da ke wakiltar jihar Kogi.
Tun da sanyin safiya ne masu zanga-zangar suka yi dirar mikiya a gaban majalisar dokokin, rike da takardu da aka yi rubuce-rubuce a kai, masu yin Allah-wadai da shugaban majalisar dattawan Sanata Bukola Saraki.
Cikin rubutun akwai wanda ke cewa, "Saraki annoba ne."
Sanata Ndume dai ya bukaci a binciki Sanata Saraki ne kan zargin shigo da mota da ya yi kasar ba bisa ka'ida ba da Sanata Dino Melaye kan zargin sa da amfani da takardar shaidar digiri na bogi.
Dakatar da shi din da aka yi na nufin ba zai sake shiga majalisar ba, kuma ba za a biya shi dukkan alawus din da ya saba karba ba.
Daga Rariya
Title :
Ana Zanga-zangar Nuna Adawa Da Dakatar Da Sanata Ndume
Description : Daruruwan masu zanga-zanga sun taru a kofar shiga majalisar dokoki, da ke babban birnin tarayya Abuja, inda suke neman a janye dakatarwar d...
Rating :
5