Daga Rariya
'Yan Nijeriya kullum sai fitowa ake da abubuwan da za su dauke mana hankali, daga wannan sai wannan.
Bayan da Shugaban Majalisar Dattijai ake zargin ya yi yunkurin shigowa da wata mota kirar alfarma, abin ya ci tura inda ya samu turjiya daga jami'an kwastan saboda rashin bin ka'ida wajen shigowa da ita da kuma kokarin kin biyan haraji. Da na gaba ake gane zurfin ruwa.
Ba da jimawa ba sai kuma muka ji wani Sanata shi ma ya shigo da kwantena guda talatin ta shinkafa ta ruwa, amma kuma aka ce yis ne, inda zakakuran jami'an kwastan suka gano cewa shinkafa ce. Shi ma dai yana neman kaucewa biyan harajin.
Yau kuma mun samu labarin wani Sanatan shi ma daga Kano ya shigo da motoci ta barauniyar hanya, inda ya zuwa yanzu aka kama guda goma sha uku.
Shin da haka kuke da ran za ku yi doka a bi bayan kuma baku girmama dokar?
Shin ko wannan ne sanadiyyar fadan ku da shugaban kwastan?
Matukar dai irin wadannan ne shugabanni, to za a cigaba da samun matsala.
Ko me ya sa kasar nan kullum muna da labarin dadawa?
Title :
Yadda Ake Yawo Da Hankalin 'Yan Nijeriya
Description : Daga Rariya 'Yan Nijeriya kullum sai fitowa ake da abubuwan da za su dauke mana hankali, daga wannan sai wannan. Bayan da Shugaban Ma...
Rating :
5