Katafaren kamfanin shirya finafinan Hausan nan, wato G.G Production ya zo da sabon salo a masana'antar fim, inda zai kashe kimanin naira milyan goma a wani sabon fim din sa mai suna 'Gudun Tsira' wanda za a soma daukarsa nan ba da jimawa ba.
A yayin kaddamar da labarin fim din a 'Tea Palour' dake kan Titin Korau a unguwar Lamido Cresent dake yankin karamar hukumar Nassarawa, a birnin Kano, shugaban kamfanin na G.G Production, Nuhu Abdullahi wanda shi ma jarumi ne a masana'antar, ya bayyana cewa, fim din zai mayar da hankali ne kan al'amuran da suke tattare da illar tukin ganganci musamman a wannan kasa ta mu Nijeriya. Sannan kuma ya qara da cewa za a soma daukar fim din ne a ranar 28 ga watan Maris, 2017. Sannan kuma za a kai aqalla makonni biyu da kwana uku ana daukar fim din.
"Mun yi nazari ne kan yadda ake yi wa tuqin ganganci a cikin al'umma kasar nan, don haka muka ga ya ya kamata mu bayar da namu gudummawar don wayar da kan dirobobi game da illar dake tattare da tukin ganganci", cewar Nuhu.
Matashin jarumin wanda kamfaninsa na G.G Production ne ya shirya finafinai irin su 'Baya Da Kura', da 'Ana Wata Ga Wata' da sauransu, ya kuma qara da cewa yana da tabbacin cewar da zarar fim xin ya shigo kasuwa zai taimaka matuqa wajen rage yawan hadduran abeben hawa a kasar nan. Domin duk wanda yake tuka mota ko babur, idan yana tukin ganganci sai ya gyara da zarar ya kalli fim din.
Game da yadda ake kuka a masana'antar shirya finafinai cewa harkar kasuwancin fim ya dan ja baya amma sai ga shi za a kashe irin wannan milyoyin kuxin don shirya wannan fim din, an tambayi Nuhu ko ta yaya yake ganin za a mayar da kudin wannan fim din?
Sai jarumin ya ce "duk wasu hanyoyi da muka san za mu bi don sayar da fim xin har a mayar da wannan kuxin tare da samun riba, mun riga mun bi su. Kamar ta bangaren 'You tube da ma yadda za mu kai wa mutum fim xin har gida idan yana bukata. Don haka duk hanyoyin da ya kamata mu bi don kaucewa barayin zaune mun riga mun bi".
Nuhu ya qara da cewa nan gaba a duk lokacin da zai yi fim dinsa, zai hada taro makamancin haka domin hada kan jaruman da za su fita a fim din. Saboda kowa ya san matsayinsa a fim din.
Nuhu ya kuma yi wa masu kallo albishir da cewa fim din zai zo da sabon salo wanda ba su taba ganin irin sa ba a finafinan Hausa.
An dai shirya taron ne domin haxa kan jaruman da za su fito a fim din.
Wasu daga cikin jaruman da za su haska a fim din, sun hada da Ali Nuhu, Nuhu Abdullahi, Falalu Dorayi, Yusuf Haruna (Baban Chinedu), Hadiza Aliyu Gabon, Jamila Umar Nagudu da sauransu. Sannan kuma Falalu Dorayi shi zai bada umarni, yayin da kuma shahararren marubucin nan, Ibrahim Birniwa ya tsara labarin. Nazi Yakasai kuma shi zai shirya fim din.
A yayin tofa albarkacin bakinsa, jarumi Ali Nuhu ya nuna jin daxinsa kasancewarsa cikin jaruman da za su haska a fim din kasancewar babban fim ne wanda kowane jarumi zai yi alfahri da shi.
Haka su ma sauran jaruman fim xin kamar su Jamila Nagudu da Hadiza Gabon sun nuna farin cikinsu a matsayin su na waxanda za su haska a cikin shirin.
Tun da farko dai shahararren dan wasan barkwancin nan kuma mai tace finafinai, wato Ali Artwork, ya nishadantar da ximbin jama'ar da suka halarci taron.
Bayan kamalla taron an shiga sashen cin abinci inda kowa ya cika cikinsa daga bisani aka tashi daga taron da misalin karfe daya na rana.
Shi dai wannan katafaren fim din da ake shirin soma xaukarsa, ya zo ne a dai lokacin da ake kokarin ganin an bunkasa harkar kasuwancin finafinai, inda ya kamata a ce ana haska finafinan Hausa a manyan sinimomi kafin a sake su su shiga kasuwa kamar yadda sauran farfajiyar shirya finafinai na duniya suke yi. Inda ake ganin tamkar ci baya ne a dinga yawo da kwafen finafinai a kan titi ana saida su kan farashin naira dari biyu.
Title :
Photos: Nuhu Abdullahi Zai Kashe Naira Milyan Goma A Sabon Fim Dinsa Mai Suna Gudun Tsira
Description : Katafaren kamfanin shirya finafinan Hausan nan, wato G.G Production ya zo da sabon salo a masana'antar fim, inda zai kashe kimanin nair...
Rating :
5