Wata babbar kotu a Abuja, ta bayar da belin tsohon shugaban kamfanin man fetur na, NNPC, Andrew Yakubu.
Kotun ta bayar da belinsa ne a kan naira miliyan 300, ya kuma gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa, wadanda suka mallaki kadarori a Abuja, babban birnin kasar.
A watan da ya gabata ne hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, ta kama Mista Yakubu, sakamakon gano miliyoyin daloli a wani gidansa a Kaduna.
Title :
Kotu Ta Bada Belin Andrew Yakubu
Description : Wata babbar kotu a Abuja, ta bayar da belin tsohon shugaban kamfanin man fetur na, NNPC, Andrew Yakubu. Kotun ta bayar da belinsa ne a kan...
Rating :
5