An gano gawar wani mai matsakaicin shekaru a rataye jikin wata bishiya a wani kauye da ake kira Tsamiya a karkashin karamar hukumar Gezawa a jihar Kano.
Saidai ana zargin mutumin ya halaka kansa ne bisa wani dalilin da ba a tabbatar ba, kamar yadda shedun gani da ido suka tabbatar.
"Mutumin ya ajiye rigarsa, takalmansa da carbinsa a karkashin bishiyar sannan ya rubuta sunansa (Nura) kafin ya kashe kansa", kamar yadda ganau ya shaida.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto gawar mutumin na sakale a jikin bishiyar.
Title :
Photos: Wani Mutum Ya Kashe Kansa Ta Hanyar Rataya A Jihar Kano
Description : An gano gawar wani mai matsakaicin shekaru a rataye jikin wata bishiya a wani kauye da ake kira Tsamiya a karkashin karamar hukumar Gezawa ...
Rating :
5