Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da hukuncin da wata kotun kasar ta yanke, da ta dakatar da umarnin da ya bada na haramtawa wasu 'yan kasashe 7 da musulmai suka yawa shiga kasar.
Mista Trump ya yi ta wallafa wasu bayanai a shafinsa na tweeter, inda ya ke cewa, hukuncin da alkalin kotun ya yanke, ba zai yi wani tasiri ba kuma shirme ne kawai.
Ya kuma kara da cewa akwai hadarin gaske, matukar za a bari mutane su yi ta kwarara Amurka.
Amurkawa da dama ne dai suka fito tituna dan nuna adawa da matakin Mista Trump tare da yin kalaman batanci a gare shi. Ana saran Amurkawa za su sake yin wata zanga-zangar a birnin Washington, da Miamai da sauransu.
A bangare guda kuma yawancin kamfanin jiragen sama sun ci gaba da dauko fasinjojin kasashen da aka hana din. Tun lokacin da yake yakin neman zabe, Mista Trump ya yi alkawarin zai kawo karshen kwararowar baki 'yan cirani kasar.
Da alkawarin gina katanga tsakanin Amurka da Mexico, duk dai a kokarin takaita shigowar 'yan cirani da 'yan gudun hijira kasar. Da alwashin haramtawa musulmai shiga Amurka, wanda hakan ya fusata wasu 'yan kasar da suke ganin ya yi wa kundin tsarin mulki karan tsaye. Wanda bai amince a fifita wani addini kan wani ba, ko mai da wani addini saniyar ware.
Title :
Shugaban Amurka Ya Yi Fatali Da Hukuncin Kotu Kan Tsangwamar Musulmi
Description : Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da hukuncin da wata kotun kasar ta yanke, da ta dakatar da umarnin da ya bada na haramtawa wasu ...
Rating :
5