Gwamnatin tarayya ta kara yawan tuhumar da take yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki bisa zargin da ake yi masa na kin bayyana adadin kadarorin da ya mallaka.
Rahotanni daga kotun Da'ar Ma'aikata (CCT) sun nuna cewa an sanya ranar 23 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da za a ci gaba da sauraren karar. Ana tuhumar Saraki ne da kin bayyana kadarorinsa a tsakanin shekarun 2003 zuwa 2011 a lokacin yana Gwamnan Kwara sannan kuma ya karbi albashin matsayin Gwamna bayan shekaru hudu da barin mulki.
Title :
Gwamnati Ta Kara Yawan Tuhumar Da Take Yi Wa Saraki
Description : Gwamnatin tarayya ta kara yawan tuhumar da take yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki bisa zargin da ake yi masa na kin bayyana a...
Rating :
5