'
'Yan kungiyar kato da Gora sun samun nasarar Bindige wasu mata uku 'yan kunar bakin wake a yayin da suke kokarin shiga kasuwar garin Gulak da ke karamar hukumar Madagali a jihar Adamawa.
Shugaban Karamar Hukumar Madagali, Alhaji Yusuf Mohammed ya ce 'yan kato da gorar sun hango Matan ne daga nesa kafin su iso kasuwar inda aka umarce su kan su tsaya amma kuma suka ki bin umarnin wanda harbin da aka yi wa mata biyu daga cikinsu, ya tayar da bama bamai da suka boye a Jikinsu.
Title :
Yan Kato Da Gora Sun Bindige 'Yan Kunar Bakin Wake Uku A Adamawa
Description : ' 'Yan kungiyar kato da Gora sun samun nasarar Bindige wasu mata uku 'yan kunar bakin wake a yayin da suke kokarin shiga kasuwa...
Rating :
5