Tun bayan tafiya hutun shekara na kwanaki 10 da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi zuwa birnin London, a kullum mutane da daman gaske na kira na don jin halin da Shugaban Kasar ke ciki.
"Bashir ya jikin Baba?" Wannan ita ce irin tambayar da mafi yawan masu kiran nawa ke yi min.
Shugaba Buhari na cikin koshin lafiya, ya London ne ba don rashin lafiya ba, sai don yayi hutunsa na shekara, kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya bashi dama, kamar yadda ya rubutawa Majalisar Tarayya.
Abin da wasu mutanen suka kasa ganewa shi ne, idan Shugaba Buhari ba shi da lafiya menene ribar mu idan muka boyewa 'yan Nigeria, alhali mun san cewa shi dan Adam ne kamar kowa, mutane ya kamata su gane cewa idan Baba Buhari ba shi da lafiya ai fitowa zamu yi mu nemi miliyoyin masoyansa su taya shi da adduar samun sauki, amma ba mu boye ba.
Masu yada irin wannan jita - jita kuma su sani cewa shi rai daya ne, kuma a hannun Allah yake, iko ne na Allah ya fara dauke masu yada jita - jitar kafin ya dauki ran Shugaba Buharin. Sau daya irin haka ta sha faruwa, idan muka dan yi bincike zamu fahimci hakan.
A karshe, a matsayin na maitaimakawa Shugaba Muhammadu Buhari kan Sababbin Kafafen Yada Labarai, zan yi amfani da wannan dama na tabbatarwa 'yan Nigeria musamman masoyan Shugaban Kasa wadanda irin wannan jita - jita ke tayar musu da hankali cewa Baba Buhari yana nan cikin koshin lafiya, kuma hutunsa na tafiya kamar yadda aka tsara, zai dawo Nigeria ranar 6th February, da yardar Allah.
Nagode
Bashir Ahmad
P.A New Media
Title :
SHUGABA BUHARI NA CIKIN KOSHIN LAFIYA
Description : Tun bayan tafiya hutun shekara na kwanaki 10 da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi zuwa birnin London, a kullum mutane da daman gaske na kira n...
Rating :
5