Mambobin Majalisar Dattawa karkashin jam’iyyar APC sun tsige Sanata Ali Ndume daga mukaminsa na shugaban gungun masu rinjaye a majalisar.
Shugaban Majalisar Dattawan ne Sanata Bukola Saraki ya karanta wasikar da jiga-jigan APC suka aiko masa da ke kunshe da bayanin tsige Ndume.
Wasikar ta bayyana Ahmed Lawan daga jihar Yobe a matsayin wanda zai maye gurbin Ndume kamar yadda Saraki ya karanta.
A lokacin da ya ke ganawa da manema labarai, Mr. Ndume ya bayyana kaduwarsa da matakin jiga-jigan APC na sauke shi daga kujerarsa, yayin da ya ce ba shi da masaniya game da makasudin tsige shi .
Sai dai ana zaton matakin tsigewar nada nasaba da zargin cin rashawa da ake yi wa Sakataren gwamnatin kasar Babachir Lawal da kuma kin tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, wato EFCC.
Ana saran majalisar za ta tabbatar da nadin Ahmed Lawan a matsayin sabon shugaban gungun masu rinjayen a zamanta na gaba.
Daga Rariya
Title :
Sanatoci Karkashin Jam'iyyar APC Sun Tsige Ndume A Matsayin Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisa
Description : Mambobin Majalisar Dattawa karkashin jam’iyyar APC sun tsige Sanata Ali Ndume daga mukaminsa na shugaban gungun masu rinjaye a majalisar....
Rating :
5