Daga Jaridar Rariya
Sanata Shehu Sani, shugaban kwamitin sanatoci akan matsalar take hakkin bil'adama, a yankin arewa maso gabashin kasar nan, ya kalubalanci shugaban kasan Nijeriya Muhammadu Buhari da yin amfani da fiska biyu yayin fada da rashawa.
Sanata Sani ya yi magana ne bayan wasikar shugaba Muhammadu Buhari wanda ya aikawa majalisan dattawa inda ya wanke sakataren gwamnatin tarayya Babacir Lawal daga zargin rashawa.
"Idan aka zo yakan rashawa a majalisan tarayya da ma'aikatar shari'a, shugaban kasa yana amfani da fiya-fiya amma idan abun yazo akan 'yan majalisar zartaswa, shugaban yana amfani da hayaki." Inii shehu Sani.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin wasikan da ya aika wa majalisa, wanda aka karanta yayin zaman majalisa, ya zargi kwamitin da rashin bawa Sakataren Gwamnatin Tarayya sauraro da kunnen adalci inda Buhari ya yi nuni da cewa rahoton kwamitin ya samu rattaba hannun mutum uku ne kacal daga cikin mutane tara na kwamitin.
Amma Shehu Sani yace wasikar Buhari ya ta'allaka ne akan rashin sanin hakikanin abundq ke faruwa da kuma boye gaskiya daga makusantan shi.
Yace "Abun ya ba ni mamaki ace wannan wasika ta fito daga fadar shugaban kasa tattare da rashin sani, da kuma toshe gaskiya. Sun yi karya cewa kwamitin bata gayyaci Babacir Lawal ba. Kwamitin ta gayyace shi kuma akwai wasika da aka aika wa sakataren dindindin na ofishin Babacir" inji Shehu Sani.
Title :
Sanata Shehu Sani Ya Kalubalanci Buhari
Description : Daga Jaridar Rariya Sanata Shehu Sani, shugaban kwamitin sanatoci akan matsalar take hakkin bil'adama, a yankin arewa maso gabashin kas...
Rating :
5