A yayin da wa'adin da Kungiyar ECOWAS ta ba Shugaban Gambiya mai barin Gado, Yahya Jammeh ke karatowa na ko mika mulki ga zababben Shugaban kasar Adama Barrow ko kungiyar ta yi karfi soji, rundunar Sojan kasar ta fito fili ta nuna a shirye take ta kare Shugaban kasar daga duk wata barazana daga waje.
Wannan batu na zuwa ne a daidai lokacin da Iyalan shugaban hukumar zaben kasar Gambia, suka tabbatar da cewa ya buya ba a san inda ya shiga ba. Wasu rahotanni sun bayyana cewa Alieu Momar Njai ya arce daga kasar, saboda an fara yi masa barazana tun bayan da ya sanar da shan kayen Shugabar Yahya Jammeh a zaben da ya gabata.
Da farko dai Mista Jammeh ya amince da shan kaye inda ya taya Adama Barrow, wanda ya yi nasara murna.
Amma daga bisani ya tubure ya ce bai amince da sahihancin sakamakon zaben ba.
Jami'an tsaro sun mamaye hedikwatar hukumar zaben jim kadan bayan da Mista Jammeh ya sanar da shawararsa ta kin amincewa da sakamakon. Tarayyar Afirka da Ecowas da Majalisar Dinkin Duniya sun ce lallai ne Mista Jammeh ya mutunta kundin tsarin mulkin kasar ta Gambia. A ranar 19 ga watan Janairu ne wa'adin Mista Jammeh, wanda ya hsafe shekara 22 yana mulki, zai zo karshe.
Title :
Rundunar Sojan Gambiya Ta Marawa Jammeh Baya
Description : A yayin da wa'adin da Kungiyar ECOWAS ta ba Shugaban Gambiya mai barin Gado, Yahya Jammeh ke karatowa na ko mika mulki ga zababben Shug...
Rating :
5