Daga Mukhtar A. Haliru Tambuwal
Gwamna Aminu Tambuwal ne ya sanar da hakan, a lokacin bukin rufe gasar musabaka karo na talatin da daya a garin Tambuwal.
Haka Tambuwal ya kara da cewa Gwamnatin jihar Sokoto za ta gina makarantun renon yara na islamiya da wadansu makarantun tsangaya islamiyya da ake gwamaya karatun boko cikin su kimanin dari hudu da tamanin da takwas. Yace za a yi hakan ne domin a gwamaya karatun boko da na kur'ani.
Idan dai baku manta ba kwanan baya gwamnatin jihar ta Sokoto ta daukaka darajar wadansu makarantun islamiyya na al'umma guda goma sha biyar zuwa na mata domin inganta koyarwa a wadannan makarantu.
Gwamna Tambuwal ya kuma yi alkawarin ci gaba da yin duk abin da ya dace domin bunkasa ilmin addini da kuma sha'anin musabaka a jihar Sokoto.
Haka zalika za a ci gaba da ginawa, gyara da kuma fadada makarantun islamiyya da masallatai a fadin jahar. Ya bayyana cewa bada dadewa ba ya sanyawa wata doka hannu ta amincewa kwamitin zakka da wakafi ya koma hukuma domin inganta ayukkan su, a kuma ragewa wa mabukata wahalhalun yau da kullum.
Da yake jawabi Mai Alfarma Sarkin Musulmi wanda sarkin yakin Binji Alh Kabiru Usman Abdulwahab ya wakilta, ya ba da tabbacin ci gaba da bada goyon bayan shi wajen inganta shaanin musabaka da hardar Qurani. Ya jinjinawa gwamntin jaha kan kudurinta na ba sashen ilimi kulawar da ya kamata.
A nashi jawabi kwamishinan ilimi na matakin farko da sakandare, Dakta Moh'd Jabbi
Kilgori, ya yabawa gwamntin jihar kan goyon bayan da take bayarwa wajen ingantawa da bunkasa ilimi a jihar, wanda ya sa kwalliya na biyan kudin sabulu kasancewa duk lokacin da yan asalin jihar suka je gasar musabaka sukan dawo da nasara da kyautar da suka ci.
Ya yi kira ga shugabannin kananan hukumomi da su ba jamian musabaka na yankunan su goyon bayan da ya kamata domin a zakulo yara masu hazaka da za su wakilci jahar.
Wadanda suka lashe kyautar gwarzon shekara a gasar dai sune Lukman Umar daga Wamakko a bangaren maza sai Zainab Aliyu Gidan Kanawa daga Sokoto Ta Kudu? a bangaren mata wadanda suka lashe bangaren hizif sittin da tajweed da tafseer.
Kowannen su dai ya samu kyautar naira miliyan daya da kujerun aikin hajji su da mahaifansu wanda gwamna Tambuwal ya ba su, Mai Alfarma Sultan ya ba namijin babur macen kuma an ba ta gado da kujeru. Suma wadanda suka lashe gasar hizif sittin ba tare da tajweed ba Gwamna Tambuwal ya ba su kujerin makka.
Shi ma wanda ke kula a gasar musabaka, Malam Bello Abdulhakim Galadanci Gwamna ya bashi mota. A yayin da kwamishinan lamurran addini, Mani Maishinko ya ba dukkanin ko'odinetocin musabaka na kananan hukumomi 23 babura domin su ci gaba da gudanar da aikin su yadda ya kamata.
Sauran wadan da suka ci nasara a hizif goma da ishirin da arba'in suma sun samu kyautar kudi.
Title :
Photos: Gwamna Tambuwal Ya Baiwa Gwarazan Musabakar Bana Ta Jiha Miliyoyin Nairori Da Kujerun Hajji
Description : Daga Mukhtar A. Haliru Tambuwal Gwamna Aminu Tambuwal ne ya sanar da hakan, a lokacin bukin rufe gasar musabaka karo na talatin da daya a...
Rating :
5