Sabbin Rahotanni sun bayyana game da yadda sojoji suka kwace Dajin Sambisa daga hannun mayakan Boko Haram. Wata majiyar mai karfi daga rundunar soja wadda ke da alhakin mamaye Dajin ta bayyana cewa a mako daya kafin kaddamar da harin, an ba sojojin Nijeriya da na Kamaru umarnin kasancewa cikin shiri bayan sun kai daf da hedkwatar kungiyar wanda aka fi Sani da sansanin ' Camp Zero'.
A cewar majiyar, mayakan Boko haram da ke sansanin suna samun ruwan sha ne a wata gonan rani da ke Alapo a cikin Dajin wanda kuma a tsakanin wannan lokaci da sojojin ke jiran umarni kai farmaki, sukan yi arangama da mayakan Boko Haram din idan sun zo dibar ruwan sha a gonar kasancewa dukkan bangarorin biyu sun dogara da gonar ce wajen samun ruwan sha.
Majiyar ta ci gaba da cewa an sake ba sojojin wa'adin kwanaki bakwai na su kasance cikin shiri kafin an tantance yanayin sansanin wanda a cewar majiyar a cikin wadannan kwanakin ne kwamandojin kungiyar wanda ya hada da Shugabansu, Shekau suka samu damar sulalewa daga sansanin. Majiyar ta kara da cewa a lokacin da sojoji su farma sansanin sun tarad da duk mayakan sun arce.
Majiyar ta kuma bayyana cewa sojojin sun samu tsoffi da kananan yara sai wasu bindigogi kirar AK47 da kuma wasu tankokin yaki da suka rigaya suka banka masu wuta. Sauran abubuwan da sojojin suka samu a sansanin sun hada da tufafi, tukwanen dafa abinci, kayayyakin abinci, babura, na'urorin sanyaya abinci wato Fridges, janaretoci da Katihun kwanciya. A gefen sansanin akwai Kaburbura wadanda ake ganin na wasu daga cikin shugabannin kungiyar ne.
A cewar Majiyar a halin yanzu dai, Shugaban Kungiyar, Shekau yana tare da manyan Kwamandojinsa sai ana ganin bai tare da sauran 'yan Matan Chibok saboda yanayin da ya arce daga sansanin. Majiyar ta ce wannan ba shi ne karon farko da aka taba kwace sansanin ba,ma shekarar 2013, sojoji sun kwace shi amma daga baya suka janye sai dai majiyar ta tabbatar da cewa sojoji za su ci gaba da tsefe dajin don farautar mayakan.
Title :
Photos: Ainihin Abin Da Ya Faru A Dajin Sambisa Yayin Fatattakar Boko Haram - Bincike
Description : Sabbin Rahotanni sun bayyana game da yadda sojoji suka kwace Dajin Sambisa daga hannun mayakan Boko Haram. Wata majiyar mai karfi daga rund...
Rating :
5