A Yau Ne 'Yan Matan Suka Cika Shekaru 1000 A Hannun 'Yan Boko Haram
* Ba Da Jimawa Ba Za Mu. Ceto Sauran Matan- Buhari
___________¥__________
A yau Lahadi ne ake cika kwanaki 1000 da sace 'yan matan na makarantar Chibok 276 da mayakan Boko Haram suka yi a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nigeria.
Lamarin dai ya ja hankalin mutane da gwamnatoci a sassan duniya daban-daban; inda aka yi ta yin zanga-zangar neman a sako su.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce yana fata nan ba da jimawa ba za a ceto sauran 'yan matan Chbok da aka sace kwana 1000 da suka wuce. Shugaba Buhari, wanda ya bayyana haka a shafinsa na Twitter ranar Lahadi, ya kara da cewa gwamnatinsa tana bakin kokarinta domin ganin ta ceto 'yan matan da ma sauran mutanen 'yan Boko Haram suka sace.
A cewarsa, " Ina so na jaddada matsayina cewa kamar yadda a baya na sha alwashin ceto su, yanzu ma ba za mu karaya ba har sai mun mayar da sauran 'yan matan hannun iyayensu". Shugaban na Najeriya ya jinjina wa dakarun sojin kasar bisa jajircewarsu wajen yaki da Boko Haram, yana mai yaba wa dukkan mutanen da ke fafutikar ganin an ceto 'yan matan.
Title :
Matan Chibok Sun Cika Kwanaki Dubu A Hanun Yan Boko Haram
Description : A Yau Ne 'Yan Matan Suka Cika Shekaru 1000 A Hannun 'Yan Boko Haram * Ba Da Jimawa Ba Za Mu. Ceto Sauran Matan- Buhari ___________...
Rating :
5