Mata a kasashen Australia da New Zealand da kuma Japan sun fara gudanar da zanga-zangar kin jinin Shugaban Amurka Donald Trump.
Wannan na zuwa ne sa'o'i gabanin wani maci na mata miliyan daya da aka shirya yi nan gaba a ranar Assabar a birnin Washington domin nuna adawa da ra'ayin Shugaba Trump na rashin ganin kimar mata.
Zanga-zanga mafi girma kawo yanzu ita ce wadda ke gudana a birnin Sudney na Australia inda kimanin mutane 3000 suka yi maci zuwa ofishin jakadancin Amurka suna caccakar Mr. Trump kan nuna halayyar raina mata.
Rahotanni sun ce an shirya yin irin wannan macin a wurare 700 a sassa daban-daban na duniya ranar Assabar din.
Title :
Mata Sun Fara Zanga-zangar Kin Jinin Trump A Kasashen Duniya
Description : Mata a kasashen Australia da New Zealand da kuma Japan sun fara gudanar da zanga-zangar kin jinin Shugaban Amurka Donald Trump. Wannan na z...
Rating :
5