A wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na ma'aikatar ilimi ta jahar Katsina Alhaji Salisu Lawal Kerau, ya sanyawa hannu ya rabawa manema labarai ta bayyana cewa Gwamna Aminu Bello Masari ya amince da gina makarantu sakandiren sojoji guda biyu ta maza da mata a Katsina.
Sanarwa ta kara da cewa makarantu za'a gina guda a Karamar Hukumar Faskari wadda ta maza ce zalla, a yayin da za'a gina ta 'yan mata a garin Barkiya dake Karamar Hukumar Kurfi. Haka kuma dukkansu na kimiyya ne.
Kamar yadda sanarwa ta ce wadannan makarantu suna karkashin kulawar rundanar sojojin Nijeriya. Kuma tuni shirye-shirye sun yi nisa na ganin an fara karatu a makaranta 'yanmatan dake garin Barkiya.
Idan za'a iya tunawa a kwanaki baya ne Gwamna Aminu Bello Masari ya amince da kafa makarantar sakandire ta Jami'an Tsaron Farin Kaya Wato (DSS) a Karamar Hukumar Musawa. Daman akwai Sakandiren 'Yan Sanda ta maza dake Karamar Hukumar Mani.
Title :
Masari Ya Amince Da Kafa Sakandiren Sojoji Guda Biyu A Katsina
Description : A wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na ma'aikatar ilimi ta jahar Katsina Alhaji Salisu Lawal Kerau, ya sanyawa hannu ya r...
Rating :
5