Kakakin kungiyar PENGASSAN, Emmanuel Ojugbana, wanda ya shaida wa majiyar mu hakan, ya kara da cewa sun dauki matakin ne saboda kamfanonin man da suke yi wa aiki ba sa aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla kan jin dadin ma'aikata.A cewarsa, za su tattauna da ministan kwadagon kasar Chris Ngige domin ya shiga tsakaninsu da kamfanonin man.
Yajin-aikin dai zai yi tasiri wajen hako da fitar da man fetur da iskar gas.Kungiyoyin ma'aikatan man dai sun dade suna yajin-aiki a Najeriya, akasari domin su matsa a aiwatar da wasu matakai da suke son ganin an dauka.Sai dai 'yan kasar da dama na ganin yajin-aiki ba shi ne mafita ba.A wani labarin kuma, Ana ci gaba da fuskantar karancin man kalanzir da kuma iskar gas a jihojin Najeriya, in da a halin yanzu ake siyar da lita guda ta kalanzir a kan Naira 300 ko fiye da haka, yayin da farashin iskar gas shi ma ya tashi sama. Rahotanni daga sassan kasar dai sun tabbatar da yadda matsalar ta jefa jama'a cikin mawuyacin hali.
Daga Naij Hausa
Title :
Ma'aikatan Mai Sun Shiga Yajin-Aiki
Description : Kakakin kungiyar PENGASSAN, Emmanuel Ojugbana, wanda ya shaida wa majiyar mu hakan, ya kara da cewa sun dauki matakin ne saboda kamfanonin m...
Rating :
5