Wata 'yar majalisar dokoki a kasar Kenya ta tsaya tsayin daka domin mata su hana mazansu damar yin jima'i matukar ba su yi rijistar zabe ba.
A ranar Litinin ce Mishi Mboko, mai wakiltar Mombasa ta bukaci matan kasar su hana mazansu kwanciyar aure domin tursasa musu karbar katin zabe a zaben da za a yi na watan Agusta.
A lokacin da take jawabi a wurin wani taro a filin Kenyatta da ke Mkomani a Mombasa inda ta raba wa kungiyoyin mata da matasa cekin kudi, Ms Mboko ta ce jima'i abu ne mai matukar muhimmanci da zai sa maza su gaggauta yin rijistar zabe da zarar sun ji cewar za a hana su.
Mijin Mboko dai ya tsira daga wannan mataki da matan kasar ke shirin dauka a kan mazajensu saboda ya riga ya yi rijista.
Ta ce " wannan ita ce hanya mafi kyau, ku hana su jima'i har sai sun nuna muku rijistar zabensu.
Ta kara da cewa lokaci ya yi da ya kamata mata su yi amfani da jima'i domin su karfafawa mazan nasu gwiwa domin su dauki rijistar masu zabe da muhimmanci idan dai har jam'iyyar adawa na fatan yin nasara a zaben da za a yi.
Title :
Kin Yin Rajistar Zabe Na Neman Jefa Maza Cikin Jangwan A Kenya
Description : Wata 'yar majalisar dokoki a kasar Kenya ta tsaya tsayin daka domin mata su hana mazansu damar yin jima'i matukar ba su yi rijistar...
Rating :
5