Martanin na Iran ya zo ne bayan da Donald Trump ya sa hannu kan dokar da ke haramta wa musulmi daga kasashe 7 da suka hada har da kasar ta Iran izinin shiga cikin kasar Amurka, inda Iran ita ma a nata bangaren ta kafa dokar da ke haramta wa duk wani dan kasar Amurka shiga cikin kasarta.
Bayanin wanda ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar a jiya Asabar, ya yi nuni da cewa wannan matakin da Trump ya dauka da zimmar cin zarfin muuslmi da kuma tozarta su, ya yi hannun riga da dukkanin dokoki na kasa da kasa da ka’idoji da matakai na diflomasiyyah.
Haka nan kuma bayanin ya ce Trump ya dauki wannan mataki ne bisa babatun da yake yi da sunan kare Amurka daga abin da yake kira ayyukan ta’addancin musulmi, alhali hakan shi ne babban abin da zai kara karfafa masu tsatsauran ra’ayi su kara kulla gaba da Amurka, ta yadda hakan zai kara saka Amurka cikin rashin aminci a duniya.
Dangane da batun hana Iraniyawa izinin shiga kasar Amurka kuwa, Bayanin ya ce hakan ya karyata ikirarin da Amukra take yi na cewa tana gaba da gwamnatin Iran ne kawai ba al’ummar kasar ba, domin kuwa wannan doka ta shafi dukkanin al’ummar Iran ne baki daya.
A ranar Juma’ar da ta gabata shugaba Hassan Rauhani ya caccaki shugaban kasar ta Amurka a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a gaban wani taro a birnin Tehran, inda ya gargadi Trump dangane da bin son ransa wajen aiwatar da siyasar kasarsa, tare da bayyana cewa lokacin sa shingayen wariya a tsakanin al’ummomi ya wuce.
Masana da dama kan harkokin siyasar kasa da kasa sun yi imanin cewa, ci gaba da aiwatar da irin wannan salo na siyasar Donald Trump, ko shakka babu zai mayar da Amurka baya, ta yadda ba za ta iya yin tinkaho a matsayin kasa mai mafi karfin fada aji ta fuskar siyasa a duniya ba, domin kuwa irin turbar da Trump ya hau za ta kawo karshen kima da haibar Amurka a duniya.
Babban misalin hakan kuwa shi ne, yadda akasarin al'ummar Amurka suke nuna adawarsu da salon siyasar Trump da ta shafi ciki da wajen kasar, inda tun kafin rantsar da shi har zuwa yau, zanga-zangar miliyoyin Amurkawa da ke nuna kin jinin siyasarsa sai kara bazuwa ta ke yi zuwa manyan biranan kasar,
ta lamarin da har ya kai ga yanzu wasu daga cikin jahohin kasar ta Amurka sun fara tunanin ballewa daga kasar domin kafa kasarsu mai cin gishin kanta, da hakan ya hada har da jahar California, jaha mafi girma a kasar Amurka, kuma daya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci da tattalin arziki mafi girma a duniya, ayin da kuma akasarin kasashen yamamcin turai masu karfin fada a ji suke nuna rashin gamsuwarsu da siyasar Trump, kuma ba su daukarsa a matsayin abokin kawance kamar yadad suka saba yi tare da sauran shgabannin da aka yi a kasar Amurka.
Daga Rariya
Title :
Gwamnatin Kasar Iran Ta Haramta Wa Amurkawa Shiga Kasarta
Description : Martanin na Iran ya zo ne bayan da Donald Trump ya sa hannu kan dokar da ke haramta wa musulmi daga kasashe 7 da suka hada har da kasar ta ...
Rating :
5