Daga BBC HAUSA
Tsohuwar Ministar albarkatun mai ta Nigeria Diezani Alison-Madueke ta mika wa gwamnatin kasar dalar Amurka miliyan 153 da ake zargin ta sata daga asusun gwamnati.
Hakan dai ya biyo bayan wani hukunci da wata kotu ta yanke a birnin Legas ranar Jumu'a cewa matar ta mika wadannan kudaden ga gwamnatin har a tabbatar da halaccinsu ko akasin haka.
A cewar hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa ta EFCC - wadda ita ce ta bukaci kotun da ta umarci tsohuwar ministar ta mika kudin - an sace kudin ne daga kamfanin mai na NNPC kana aka boye su a wasu bankuna uku da ke kasar.
Kamfanin dillancin labaran kasar NAN ya ce Alkalin kotun Muslim Hassan wanda ya ba da wannan umarnin; ya bai wa jami'an bankunan uku wa'adin kwanakki 14 su bayyana gabansa domin su kawo masa shaidar da ke nuna cewa kudin ba na sata ba ne.Yadda aka saci kudin'
A cikin bukatar neman mika kudaden wadda jami'in bincike na hukumar ta EFCC Moses Awolusi ya gabatar wa kotun, hukumar ta ce a watan Disamba na shekara ta 2014 ne tsohuwar ministar ta kira babban manajan daya daga cikin bankunan a ofishinta suka tsara yadda za a saci kudaden.
Jami'in hukumar ya yi zargin cewa Mrs Diezani Alison-Madueke ta bukaci babban manajan bankin da ya tabbatar da cewa ba a saka kudin a cikin asusun da aka san da zamansa ba kuma ba a rubuta shigar da kudin ba cikin kundin da bankin ke rubuta huldodin da ya yi ba.
Rahoton na kamfanin dillancin labaran Najeriyar dai bai fadi ko lauyoyin tsohuwar ministar suna a kotun lokacin wannan zaman ba; balle martanin da suka mayar ga wadannan zarge-zargen.
Amma dai wannan ba shi ne karon farko da ake zargin ministar da almundahana ko facaka da kudaden jama'a ba, amma kuma a kodayaushe takan musanta.
Title :
Diezani Ta Mikawa EFCC Dala Miliyan Dari Hamsin Da Uku
Description : Daga BBC HAUSA Tsohuwar Ministar albarkatun mai ta Nigeria Diezani Alison-Madueke ta mika wa gwamnatin kasar dalar Amurka miliyan 153 da ak...
Rating :
5