Shugaban cocin Katolika, John Cardinal Onaiyekan, yace ba zasu bi umurnin addu’an kwana daya da kungiyar gamayyar kiristocin Najeriya watau CAN tayi umurnin ayi game da rayukan da aka rasa a jihar Kaduna ba.
Yayinda yake bayyana dalilinsa na yin hakan, ya bayyana cewa mabiya Katolika basu bin umurnin CAN. Yace: "Ban yi imani da yin addua wani ranan takamamma ba, kayi addu’a saboda ubangiji ya tsirar da mu ,ba wai lallai a ranan 8 ga watan Junairu ba."
Kafin yanzu, sakataren kungiyar CAN, Dr. Musa Asake ya alanta ranan Lahadi,8 ga watan Junairu 2017 a matsayin ranan makokin dukkan kiristocin da suka rasa rayukansu a jihar Kaduna.
Dr Asake ya kara da cewa dukkan kiristoci su sanya bakin kaya a ranan kuma suyi addu’a sosai ga wadanda suka rasa rayukansu a kudancin Kaduna.
Amma Katolika sunce ba zasu bi umurnin nan ba da bakin shugabansu Onaiyekan. Yace : Ban san abinda zance game da shugabancin CAN ba yanzu saboda cocinmu bata cikin CAN yanzu. Bamu ma san yadda aka zabi sabon shugaban CAN din ba. Saboda haka abinda zan iya yi shine in zauna in sha kallo.
“Ban zan iya ce ma dukkan mambobina su sanya bakaken kaya su zo coci ranan lahadi ba, bamu bin umurnin CAN; kowani coci na da umurnin ta.”
Daga Naij Hausa
Title :
CAN Bata Isa Ta Bamu Umarni Ba – Cocin Katolika
Description : Shugaban cocin Katolika, John Cardinal Onaiyekan, yace ba zasu bi umurnin addu’an kwana daya da kungiyar gamayyar kiristocin Najeriya watau ...
Rating :
5