Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce yana fata nan ba da jimawa ba za a ceto sauran 'yan matan Chbok da aka sace kwana 1000 da suka wuce.
Shugaba Buhari, wanda ya bayyana haka a shafinsa na Twitter ranar Lahadi, ya kara da cewa gwamnatinsa tana bakin kokarinta domin ganin ta ceto 'yan matan da ma sauran mutanen 'yan Boko Haram suka sace.
A cewarsa, " Ina so na jaddada matsayina cewa kamar yadda a baya na sha alwashin ceto su, yanzu ma ba za mu karaya ba har sai mun mayar da sauran 'yan matan hannun iyayensu".
Shugaban na Najeriya ya jinjina wa dakarun sojin kasar bisa jajircewarsu wajen yaki da Boko Haram, yana mai yaba wa dukkan mutanen da ke fafutikar ganin an ceto 'yan matan.
An sake gano wata 'yar Chibok
Ziyarar 'yan matan Chibok ta bar baya da kura
A ranar Lahadi ne ake cika kwanaki 1000 da sace 'yan matan na makarantar Chibok 276 da mayakan Boko Haram suka yi a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nigeria.
Lamarin dai ya ja hankalin mutane da gwamnatoci a sassan duniya daban-daban; inda aka yi ta yin zanga-zangar neman a sako su.
'Sun cika kwana 1000 a tsare'
Fiye da 'yan mata 50 ne suka kubutar da kansu tun ranar da aka sace sun wato 14 ga watan Afrilun 2014, yayin da kawo yanzu gwamnati ta samu kwato wasu kari 23.
A cikin wata sanarwa da ta fitar kan cika kawanakki dubun da sace su, kungiyar kare hakkin biladama ta Amnesty International ta yi kira ga gwamnatin Najeriyar ta kara matsa kaimi wajen ganin ta kubutar da sauran 'yan matan, da ma wasu da ke hannun mayakan.Kungiyar ta Amnesty ta kuma yi kira ga kungiyar Boko Haram da ta kawo karshen ukubar da ta jefa 'yan matan dama sauran wadanda take rike da su, don su koma cikin iyalansu.
Amnesty ta ci gaba da cewa, ba wai tana zargin gwamnati da rashin kokari wajn kubuto da 'yan matan da ma sauran wadanda aka sace ba ne, tana so ne a kara himma saboda ba 'yan matan kadai ne a hannun mayakan ba, har ma da wasu mutane da suka hada da mata da yara.
Sai dai ta ce tana yaba wa gwamnatin kasar kwarai da gaske wajen kubutar da sauran.
Title :
Buhari Ya Sake Shan Alwashin Ceto 'Yan Matan Chibok
Description : Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce yana fata nan ba da jimawa ba za a ceto sauran 'yan matan Chbok da aka sace kwana 1000 da suka ...
Rating :
5