A yayin da yake jajantawa wadanda harin jirgin yakin Sojan Nijeriya ya rutsa da su a sansanin 'yan gudun hijira a bisa kuskure, Shugaba Muhammad Buhari ya nuna bakin ciki da da-na- sani kan faruwar lamarin.
Shugaban ya kuma yi fatan samun lafiya ga wadanda suka samu raunuka a yayin harin inda ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta taimakawa gwamnatin jihar Borno wajen tunkarar wannan abin bakin ciki sannan kuma ya nemi jama'a su kwantar da hankularsu tare da fatan samun rahama ga wadanda suka rasa rayukansu.
Wani jirgin yakin sojin saman Najeriya ne dai ya hallaka mutane 52 sakamakon ruwan bama-bamai da ya yi a kan sansanin 'yan gudun hijra a kauyen Rann na jihar Borno, bisa zargin cewa 'yan Boko Haram ne .
Ma'aikatan agaji na cikin wadanda suka samu raunuka - kungiyar bada agaji ta Red Cross ta tabbatar da mutuwar shida daga cikin ma'aikatanta. Kungiyar likitoci masu bayar da agaji ta duniya, MSF ta ce tana kula da wadanda suka jikkata guda 200.
Harin ya faru ne a kauyen Rann da ke kusa da kan iyakar Najeriya da Kamaru, inda sojoji ke fafatawa da mayakan Boko Haram. Rundunar sojin sama ta Najeriya dai ta ce al'amarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 50 tare da jikkata 100.
Title :
Buhari Ya Jajantawa Wadanda Harin Sansanin 'Yan Gudun Hijira Ya Rutsa Da Su
Description : A yayin da yake jajantawa wadanda harin jirgin yakin Sojan Nijeriya ya rutsa da su a sansanin 'yan gudun hijira a bisa kuskure, Shugaba...
Rating :
5