Daga Jaridar Rariya
Masu shigar da kara a kasar Italiya na zargin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da tsohuwar ministar albarkatun mai Diezani Alison-Madueke da karbar kudade da yawansu ya kai $1.3 biliyan.
Ana zargin Jonathan da Diezani da karbar kudin ne a wata badakalar rijiyar man da ta shafi kamfanonin mai na ENI da Shell.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce, a wasu bayanai da kotu ta tara a watan da ya gabata a birnin Milan, ta shigar da karar sunayen mutane 11 wadanda suka hada da manyan ma'aikatan kamfanonin man da kuma kamfanonin biyu.
Sunayen Jonathan wanda ya sauka daga kan mulki a shekarar 2015 da Diezani, wace ta shafe tsawon lokacin a matsayin ministarsa ta albarktun mai basa cikin jerin sunayen da aka shigar da kararsu.
Amma ana zargin sun taka muhimmiyar rawa a badakalar wanda kamfanonin mai na ENI da Shell suka karbi $1.3 biliyan na wata rijiyar mai da ke cikin teku a Najeriya a shekarar 2011.
Ba a kama su da laifi ba a hukumance kuma wadanda ake tuhumar suna da dama ta tsawon kwanaki 20 su mayar da martani a kan rahoton binciken kafin a shigar da kara a hukumance.
Title :
An Zargi Jonathan Da Madueke Da Karbar Dala Bilyan 1.3
Description : Daga Jaridar Rariya Masu shigar da kara a kasar Italiya na zargin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da tsohuwar ministar albarkatun ma...
Rating :
5